March 28, 2024
LABARAI

Munje Otal Tare Da Murja, Kawai Yan Sanda Suka Kama Ta - Mai Wushirya

Guda cikin fitattun jaruman barkwanci a shafin TikTok, Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, yace suna tare da Murja Ibrahim Kunya, a lokacin da yan sanda suka kama ta.

Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok, yace suna tare sanda wani saurayi ya kira ta, bayan sunyi waya sai ya lura kamar ranta ya baci, to daga nan ya raka ta wajen wata mai yi mata kisho ta karasa mata kitson, su dauki kayansu suka nufi otal din Tahir dake Kano.

Mai Wushirya yace, isar su ke da wuya a cikin mota, sai suka ga wasu maza sun zagaye su, dukda cewar yace ya dauka ma samarin ta ne, sai da suka nuna shaidar su ta cewa yan sanda ne, har suka tafi da ita, dukda tayi tirjiya da fari, domin yan sandan da motar gida suka zo ba ta aiki ba.

Tuni dai al'umma ke korafe-korafe akan yadda Murja ke cin karenta babu babbaka a shafin TikTok, tare da zarginta da bata tarbiyya ta koyarwar addinin musulunci.

Admin Nasara Radio

admin@nasararadio.com.ng

an admin

Follow Me:

Comments